<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yabo Ga Allahnmu, Shi Ne Mahaliccin Kome LW37</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yabo ga Allahnmu, shi ne mahaliccin kome !
 Ya raina, yabe shi, shi ne Mai Ceto, mai kiwo.
 Zo, masu ji,
 Maza da mata ku zo,
 Ku guso nan, ku yabe shi.

[V2]
 2) Yabo ga Allahnmu, mai mulkin Sama da duniya!
 Ya kiyaye mu ƙarƙashin fukafukan kansa.
 Ba ka ji ba?
 Bukatar kowa ya biya
 Ta wurin ikon ƙaunarsa.

[V3]
 3) Yabo ga Allahnmu, wanda ya tsare mu duka !
 Kullum jinƙai da alheri su kan kiyaye mu.
 Lura da kyau.
 Kome Mai Iko ya iya,
 Don ƙaunarsa a gare mu.

[V4]
 4) Ya raina duka, ka yabi Ubangiji Allah.
 Yara da manya ku zo a gabansa da waƙa.
 Bari &quot;Amin&quot;
 Shi fito bakinmu duk.
 Har abada mu yabe shi.</lyrics>
<hymn_number>37</hymn_number>
<author>from Ander Theil des Erneuerten Gesangbuch, Neander, Joachim (1650-1680)</author>
</song>